Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Fu’ad Hussain yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa za’a gudanar da taron a birnin Bagdaza kuma an gayyaci kasashe 5 masu kujerun din-din din a kwamitin tsaro na MDD taron.
Da aka tambaye shi abinda ya sa an ki gayyatar kasar Syriya, Hussain ya amsa da cewa, kasar Iraki ta na da kekyawar dangantaka da kasar Siriya amma matsalar ta da manya-manyan kasashen duniya ya sanya sarkakiya a cikin hulda da ita.
Wannan shi ne taron kasa da kasa na farko wanda kasar Iraki take shiryawa tun shekara 1990, kuma kasashe kimani 10 ne zasu halarci taron na Bagdaza, daga ciki akwai kasashen da suke makobtaka da ita wadanda suka hada da Iran, Turkiyaa, Saudiya, Kuwait da kuma Jordan.
342/